中国国际广播电台
Tun shekara aru aru , a Tudun
Emei akwai macizai biyu .
Sun yi shekaru fiye da dubu
suna zaman rayuwa a tudun.
Daya daga cikinsu farin maciji
ne . Daya daban kuma bakin
maciji ne . Saboda su biyu
suna kaunar yanayin duniyar
mutane , shi ya sa sun zama
yarinyoyi biyu masu kyaun
gani . Sunan yarinya ta farko
shi ne Bai Suzhen . Sunan
yarinya daban shi ne Xiao
Qing . Wata rana sun yi yawon
shakatawa a Tafkin Xihu da
ke birnin Hangzhou , shahararren
wuri mai ni'ima .Yanayin Tafkin
Xihu yana da ni'ima kwarai
da gaske . Da su isa wurin
kusa da Gadar Duanqiao , sai
gari ya yi durum durum , kuma
an fara yin ruwa . Su biyu
sai sun zo karkashin wani
itace , don gudun ruwa . A
daidai wannan lokaci , wani
saurayi yana zuwa kuma rike
da wata laima . Sunansa shi
Ne Xu Xian . Ya dawo daga
kabarin ba da dadewa ba .
Da ya ga yarinyoyi biyu suna
tsaya a karkashin itace ,
sai ya yi aron laimarsa gare
su , kuma ya ba da taimako
gare su don kiran wani jirgin
ruwa da kai su koma guda.
Bai Suzhen ta fara kaunar
Xu Xian , sai ta sa Xu Xian
za ta zo gidanta don daukar
laima . A kashe gari Xu Xian
ya zo gidan Bai Suzhen dake
jan ginin a bangaren tafkin
. Bai Suzhen ta gode wa XuXian
saboda ya taimake ta . Da
ta san iyayen Xu Xian sun
mutu , kuma yanzu yana zaune
a gidan kawarta , kuma yana
aiki a wani kantin magani
. Bai Suzhen ta roki Xu Xian
, su yi aure . Ko shakka babu
Xu Xian ya yi farin ciki kwarai
da gaske . Sa'an nan kuma
a karkashin jagorancin Xiao
Qing sun yi bikin aure . Bayan
da suka yi aure , sai su da
kansu sun kafa wani kantin
magani . Bai Suzhen ta kware
a wajen jiyya . Ko wace rana
tana ganin mutane masu fama
da cututtuka . Mutane suna
kaunarta sosai kuma suna kiranta
da Madam Bai .
A birnin Zhenjiang akwai
wani haikalin Jinshan . A
cikin wannan haikalin akwai
wani budda , sunansa shi ne
Fa Hai . Da ya sami labarin
cewa , Bai Suzhen wata dodon
maciji ce wadda take da shekaru
dubu . Yana tsamanin cewa
, tabbas ne kowane dodon maciji
zai lahanta mutane , sai ya
fitar da dabaru ga Xu Xian
, ya sa Xu Xian ya bar Bai
Suzhen kuma ya zama budda
.
Wata rana Fa Hai ya zo gidan
Xu Xian kuma ya gaya wa Xu
Xian cewa , matarsa ita ce
wani dodon maciji . Xu Xian
bai amince da wannan ba ,
sai Fa Hai ya koyar masa cewa
, a ran 5 ga watan Mayu ,
ya sa Bai Suzhen shan giya
, sai za ta fitar da masifarta
ta da .
Ya zuwas ranar bikin Ran 5
ga watan Mayu , kowane iyali
suna shan giya don maganin
masifa . Amma maciji yana
tsoron wannan giya . Bai Suzhen
da Xiao Qing suna tunanin
zuwa tudu don gudun bikin
. Amma tana tsoron Xu Xian
yana shakkarta.
Da aka ceci Xu Xian sai ya
yi 'dan tsoro . Bai Su Zhen
ta yi tunani da wata dabara,
sai ta yi amfani da mayani
mai launin fari don ya zama
wani farin maciji kuma ta
rataye a marufin daki , ta
bar Xu Xian gani . A wannan
lokaci , sai Xu Xian bai sake
shakkar matarsa dodon maciji
ce, kuma sun farfado da soyayya
da juna . (Ado)
|